Leviticus 11:28 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk wanda ya ɗauki gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har yamma. Waɗannan dabbobi za su zama marasa tsabta a gare ku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ وَنْدَ يَطَوْكِ مُوشٜىٰنْ إِرِنْسُ، سَيْ يَوَنْكٜىٰ رِيغُنَنْسَ، عَمَّا دُكْدَهَكَ ذَيْ ڧَظَنْتُ حَرْ يَمَّ، غَمَا سُو مَاسُ ڧَظَنْتَنٜىٰ أَغَرٜىٰكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wanda kuma ya ɗauki mushensu, sai ya wanke tufafinsa, ya zama ƙazantacce har zuwa maraice.