Leviticus 11:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Akwai waɗanda suke tuƙa ko kuwa suna da rababben kofato kawai, duk da haka ba za ku ci su ba. Waɗannan kuwa su ne, raƙumi, ko da yake yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato; saboda haka cin namansa haram ne gare ku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَثِكِنْ مَاسُ تُڧَرْ عَبِنْثِ عَبَاكِ، كُواْ مَاسُ تَڢِنْ ڧَڢَرْدَ يَرَبُ بِيُ، غَا وَطَنْدَ بَذَاكُثِبَ؞ رَاڧُمِ، كُواْدَيَكٜىٰ يَنَ تُڧَرْ عَبِنْثِ، عَمَّا بَ شِ دَ تَڢِنْ ڧَڢَرْدَ يَرَبُ بِيُ، يَذَمَ مَيْ ڧَظَنْتَا كٜىٰنَنْ أَغَرٜىٰكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ko daga cikin masu tuƙar ko masu rababben kofaton ba za ku ci waɗannan ba. Raƙumi yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, haram ne a gare ku.