Leviticus 12:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Macen da ta yi ciki ta kuma haihu ɗa namiji za tă ƙazantu kwana bakwai, kamar yadda takan ƙazantu a lokacin al’adarta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَڢَطَا وَیَیَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ وَطَنَّنْ ڧَٰعِدُواْدِ؞ «عِدَنْ مَثٜىٰ تَايِ ثِكِ تَا حَيْڢِ طَا نَمِجِ، ذَاتَ ڧَظَنْتُ حَرْ ݣُونَ بَݣَويْ دَيْدَيْ يَدَّ تَكَنْ كَسَنْثٜىٰ عَݣُونَكِنْ غَنِنْ أَلْعَادَرْتَ تَوَتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan mace ta yi ciki, ta haifi ɗa namiji, to, za ta zama marar tsarki har kwana bakwai, kamar cikin kwanakin hailarta.