Leviticus 12:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In ta haifi ’ya ta mace ce, makoni biyu macen za tă ƙazantu kamar yadda takan kasance a lokacin al’adarta. Sa’an nan dole tă jira kwana sittin don a tsabtacce ta daga zub da jininta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عَمَّا عِدَنْ تَا حَيْڢِ یَ مَثٜىٰ، ذَاتَ ڧَظَنْتُ حَرْ ݣُونَكِے غُواْمَشَا حُطُ دَيْدَيْ يَدَّ تَكَنْ كَسَنْثٜىٰ عَݣُونَكِنْ غَنِنْ أَلْعَادَرْتَ تَوَتَ؞ بَايَنْ وَنَّنْ، ذَاتَ ڧَارَ ݣُونَكِے سِتِّنْ دَ شِدَ، وَتُواْ ݣُونَكِنْ ڟَبْتَثٜىٰوَرْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma idan 'ya mace ce ta haifa, za ta zama marar tsarki mako biyu kamar a kwanakin hailarta. Za ta ci gaba da zama cikin jinin har kwana sittin da shida.