Leviticus 12:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Sa’ad da kwanakin tsabtaccewarta don ɗa namiji ko ’ya ta mace suka cika, sai ta kawo ɗan rago bana ɗaya wa firist a bakin ƙofar Tentin Sujada don hadaya ta ƙonawa da tattabara ko kurciya na hadaya don zunubi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَعَدَّ ݣُونَكِنْ ڟَبْتَثٜىٰوَرْتَ نَحَيْڢُوَرْ طَا كُواْ یَ سُكَ ثِكَ، ذَاتَ كَٰوُاْ وَ ڢِرِسْتِ طَنْ ضَغُواْ مَيْ شٜىٰكَرَا طَيَ عَبَاكِنْ ڧُواْڢَرْ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ دُواْمِنْ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا؞ ذَاتَ كُمَ كَٰوُاْ تَتَّبَرَ كُواْ كُرْثِيَ دُواْمِنْ هَدَايَ تَوَنْكٜىٰ ذُنُوبِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da kwanakin tsarkakewarta na haihuwar ɗa ko 'ya suka cika, sai ta kai wa firist ɗan rago bana ɗaya, a ƙofar alfarwa ta sujada don hadaya ta ƙonawa, da ɗan tattabara, ko kurciya na yin hadaya don zunubi.