Leviticus 12:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Firist zai miƙa su a gaban Ubangiji don yă yi kafara dominta, sa’an nan tă tsabtacce daga zub da jininta. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin macen da ta haifi ɗa namiji ko ’ya ta mace.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتِ ذَيْ مِيڧَشِ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ، دُواْمِنْ أَڟَبْتَثٜىٰ مَثٜىٰنْ؞ مَثٜىٰنْ كُوَ ذَاتَ ذَمَ مَرَرْ ڧَظَنْتَادَغَ جِنِنْتَ؞ وَنَّنْ ڧَٰعِدَ ثٜىٰ غَ دُكْ مَثٜىٰنْ دَ تَحَيْڢِ طَا كُواْ یَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya miƙa ga Ubangiji, ya yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka. Wannan shi ne abin da ya wajaba ga wanda ta haifi ɗa ko 'ya.