Leviticus 13:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Firist zai bincike shi, in kuma ya zama ya fi fatar jiki zurfi kuma gashinsa ya juya ya zama fari, firist ɗin zai furta shi marar tsarki. Cuta ce mai yaɗuwa da ta fasu a inda ƙurjin yake.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ڢِرِسْتِ يَدُدُّوبَ وُرِنْ، عِدَنْ ثُوتَرْ تَشِغَ ڢَتَرْ جِكِنْ دَ ظُرْڢِ، كُمَ غَاشِنْ وُرِنْ يَجُويٜىٰ ڢَرِ، ڢِرِسْتِ ذَيْ سَنَرْدَ مَيْ ثُوتَرْ ثٜىٰوَ شِے مَيْ ڧَظَنْتَا نٜىٰ؞ مُوغُوَرْ ثُوتَرْ ڢَتَرْ جِكِثٜىٰ تَٻَرْكٜىٰ عَثِكِنْ مَرُورُنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Firist zai dudduba shi, idan zurfin kumburin ko tabon rikiɗa fari, sai firist ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta ce ta faso a ƙurjin.