Leviticus 13:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma in sa’ad da firist ya bincike shi, ya tarar babu farin gashi a ciki, kuma bai yi zurfi fiye da fatar jikin ba, ya kuma bushe, sai firist ɗin ya kaɗaice shi har kwana bakwai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا عِدَنْ ڢِرِسْتِ يَدُدُّوبٜىٰشِ، يَغَ غَاشِنْ وُرِنْ مَرُورُنْ بَيْيِ ڢَرِ بَ، كُمَ ظُرْڢِنْ ثُوتَرْ بَيْ شِغَ حَرْ ثِكِنْ ڢَتَرْ جِكِنْسَبَ عَمَّا يَڢَارَ وَرْكٜىٰوَ، سَيْ ڢِرِسْتِ يَوَارٜىٰشِ دَغَ جَمَعَ حَرْ ݣُونَ بَݣَويْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma idan firist ya dudduba shi ya ga gashin wurin bai yi fari ba, zurfin ƙurjin kuma bai zarce fatar ba, amma ya dushe, sai firist ɗin ya kulle shi kwana bakwai.