Leviticus 13:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
firist zai bincike tabon, idan kuma gashin a cikinsa ya juya ya zama fari, kuma ya yi zurfi fiye da fatar jikin, cuta ce mai yaɗuwa da ta fasu daga ƙunan. Firist zai furta shi marar tsarki; cuta ce mai yaɗuwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ڢِرِسْتِ يَدُدُّوبَ شِ؞ عِدَنْ غَاشِنْ وُرِنْ ڧُونَرْ يَجُويٜىٰ ڢَرِ، كُمَ ظُرْڢِنْ ثُوتَرْ تَشِغَ حَرْ ثِكِنْ ڢَتَرْ جِكِنْ، تُواْ، ثُوتَرْ ڢَتَرْ جِكِثٜىٰ تَٻَرْكٜىٰ أَوُرِنْ ڧُونَرْ كٜىٰنَنْ؞ ڢِرِسْتِ ذَيْ سَنَرْدَ مَيْ ثُوتَرْ ثٜىٰوَ شِے مَيْ ڧَظَنْتَا نٜىٰ، غَمَا مُوغُوَرْ ثُوتَرْ ڢَتَرْ جِكِثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
sai firist ya dudduba shi, in gashin wurin tabo ya zarce fatar, to, kuturta ce ta faso a cikin ƙunar, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta ce.