Leviticus 13:27 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A rana ta bakwai ɗin firist zai bincike shi, in kuma cutar tana yaɗuwa a cikin fatar jikin, firist ɗin zai furta shi marar tsarki, cutar fatar jiki ce mai yaɗuwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتِ ذَيْسَاكٜىٰ دُدُّوبَ شِ أَ رَانَ تَبَݣَويْ؞ عِدَنْ ثُوتَرْ تَنَ بَظُوَ أَ ڢَتَرْ جِكِنْسَ، ڢِرِسْتِ ذَيْ سَنَرْدَ مَيْ ثُوتَرْ ثٜىٰوَ شِے مَيْ ڧَظَنْتَا نٜىٰ، غَمَا مُوغُوَرْ ثُوتَرْ ڢَتَرْ جِكِثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A kan rana ta bakwai, zai sāke dubansa, idan tabon yana bazuwa cikin fatar, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, kuturta ce.