Leviticus 13:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Firist zai bincika mikin da yake a fatar mai cutar, in gashin a mikin ya juya ya zama fari, mikin kuma ya zama kamar ya fi zurfin fatar jiki, wannan cutar kuturta ce. Sa’ad da firist ya bincike shi, zai furta shi marar tsarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتِ ذَيْ دُدُّوبَ ثُوتَرْ دَتَكٜىٰ أَ ڢَتَرْ جِكِنْ؞ عِدَنْ غَاشِنْ وُرِنْ ثِيوُانْ يَجُويٜىٰ ڢَرِ كُمَ ظُرْڢِنْ ثُوتَرْ يَشِغَ حَرْ ثِكِنْ ڢَتَرْ جِكِنْ، تُواْ، مُوغُوَرْ ثُوتَرْ ڢَتَرْ جِكِے ثٜىٰ؞ بَايَنْ ڢِرِسْتِ يَغَمَ دُدُّوبَ شِ سَيْ يَسَنَرْ دَشِ ثٜىٰوَ شِے مَيْ ڧَظَنْتَا نٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Firist ɗin zai dudduba cutar da take a fatar jikin mutumin. Idan gashin da yake wurin cutar ya rikiɗa ya zama fari, zurfin cutar kuma ya zarce fatar jikinsa, wannan cuta kuturta ce. Firist ɗin da ya dudduba shi zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne.