Leviticus 13:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In tabon a fata jikinsa fari ne amma bai zama ya fi zurfin fatar jikin ba, gashin a cikinsa kuma bai juya ya zama fari ba, firist ɗin zai kaɗaice mai cutar na kwana bakwai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا عِدَنْ ثُوتَرْ دَتَكٜىٰ أَ ڢَتَرْ جِكِنْ ڢَرِ نٜىٰ، كُمَ ظُرْڢِنْ ثُوتَرْ بَيْ شِغَ ثِكِنْ ڢَتَرْ جِكِنْبَ، غَاشِنْ دَيَكٜىٰ أَجِكِنْسَ كُمَ بَيْ جُويٜىٰ ڢَرِبَ، تُواْ، ڢِرِسْتِ ذَيْ وَارٜىٰ مَيْ ثُوتَرْ نَنْ دَغَ جَمَعَرْ حَرْ ݣُونَ بَݣَويْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma idan tabon fari ne, zurfinsa kuwa bai zarce fatar ba, gashin kuma da yake cikinsa bai rikiɗa ya zama fari ba, sai firist ya kulle mai ciwon har kwana bakwai.