Leviticus 13:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A rana ta bakwai ɗin firist zai sāke bincike shi, in kuwa mikin ya bushe bai kuwa yaɗu a fatar jikin ba, firist ɗin zai furta shi mai tsarki; ƙurji ne kawai. Dole mutumin yă wanke rigunansa, zai kuma tsarkaka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَ تَبَݣَويْ ڢِرِسْتِ ذَيْسَاكٜىٰ دُوبَنْسَ؞ عِدَنْ ثُوتَرْ تَڢَارَ وَرْكٜىٰوَ، بَاتَكُوَ بَظُو أَ ڢَتَرْ جِكِنْبَ، سَيْ ڢِرِسْتِ يَسَنَرْ دَشِ ثٜىٰوَ شِے مَرَرْ ڧَظَنْتَنٜىٰ، ڧُرَجٜىٰنٜىٰ كَوَيْ؞ سَيْ مَيْ ثُوتَرْ يَوَنْكٜىٰ رِيغُنَنْسَ، يَذَمَ مَرَرْ ڧَظَنْتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A rana ta bakwai sai firist ya sāke dubansa, idan ciwon ya dushe, cutar kuma ba ta yaɗuwa a fatar jikin mutumin, firist zai hurta, cewa, mutumin tsattsarka ne, ɓamɓaroki ne kawai, sai ya wanke tufafinsa.