Leviticus 14:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“A rana ta takwas dole yă kawo ɗan rago da ’yar tunkiya bana ɗaya, kowane marar lahani, tare da rabin garwan gari mai laushi haɗe da mai domin hadaya ta gari, da kuma moɗa ɗaya na mai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«أَ رَانَ تَتَݣُوسْ ذَيْ كَٰوُاْ یَنْ رَغُنَ بِيُ مَرَسَ تَبُواْ دَ یَرْ تُنْكِيَ مَيْ شٜىٰكَرَا طَيَ مَرَرْ تَبُواْ دَ كِلُواْ عُكُ نَغَارِنْ حَڟِ مَيْ لَوْشِ، وَنْدَ عَكَ ݣُوٻَ دَ كَشِ طَيَ ثِكِنْ عُكُ نَلِتَرْ مَنْ ظَيْتُنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A rana ta takwas zai kawo 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya marasa lahani da 'yar tunkiya bana ɗaya marar lahani, da hadaya ta gari rabin garwar gari mai laushi karɓaɓɓe da man zaitun, da rabin moɗa na mai.