Leviticus 14:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Sa’ad da firist zai ɗauki ɗaya daga cikin ragunan ya kuma miƙa shi kamar hadaya don laifi, tare da moɗan mai; zai kaɗa su a gaban Ubangiji kamar hadaya kaɗawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتِ ذَيْ طَوْكِ طَيَ دَغَ ثِكِنْ یَنْ رَغُنَ بِيُنْ، تَرٜىٰدَ مَنْ ظَيْتُنْ يَمِيڧَسُ هَدَايَ تَشَاڢٜىٰ لَيْڢِے، تَوُرِنْ مِيڧَ هَدَايَ تَطَغَوَ غَ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Firist ɗin zai ɗauki ɗan rago ɗaya ya miƙa shi hadaya don diyyar laifi, da rabin moɗa na mai, ya miƙa su don hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.