Leviticus 14:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai yanka ɗan ragon a tsattsarkan wuri inda ake yanka hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa. Gama yadda hadaya ta zunubi ta firist ne, haka hadaya domin laifi ma, hadaya ce mafi tsarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَيْ يَنْكَ طَنْ ضَغُواْنَّنْ أَوُرِنْ دَ عَكٜىٰ يَنْكَ دَبُّواْبِے نَهَدَايَ تَشَاڢٜىٰ لَيْڢِے دَ نَهَدَايَ تَڧُواْنَاوَا، وَتُواْ أَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے؞ غَمَا هَدَايَ تَشَاڢٜىٰ لَيْڢِے، كَمَرْ هَدَايَ تَوَنْكٜىٰ ذُنُوبِ، رَبُواْ نَڢِرِسْتِنٜىٰ؞ وَنَّنْ هَدَايَ تَنَدَ ڟَرْكِے سُواْسَيْ، عَيِتَ بِسَغَ ڧَٰعِدَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan zai yanka ɗan rago a inda ake yanka hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa. Tilas ya yi haka domin hadaya ta laifi rabon firist ne kamar hadaya domin zunubi. Hadaya ce mafi tsarki.