Leviticus 14:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
firist zai umarta a kawo tsuntsaye biyu masu rai, masu tsabta da itacen al’ul, jan ƙyalle da kuma hizzob saboda mutumin da za a tsabtacce.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتِ ذَيْ عُمَرْتَ عَكَٰوُاْ ڟُنْڟَيٜىٰ بِيُ مَاسُ رَيْ مَرَسَ ڧَظَنْتَادَ إِتَاثٜىٰنْ سٜىٰدَ دَ جَنْ ظَرٜىٰنْ سَاڧَ دَ غَنْيٜىٰنْ إِظُوابْ دُواْمِنْ وَنْدَ ذَاعَ ڟَبْتَثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
firist ɗin zai umarta a kawo tsuntsaye biyu masu rai, masu tsabta, da itacen al'ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya domin aikin tsarkakewa.