Leviticus 14:51 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan zai ɗauki itacen al’ul, hizzob, jan ƙyalle da kuma tsuntsu mai ran ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka da kuma cikin ruwa mai kyau, ya yayyafa wa gida sau bakwai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَيْ طَوْكِ طَيَنْ ڟُنْڟُ مَيْ رَيْ دَ إِتَاثٜىٰنْ سٜىٰدَ دَ جَنْ ظَرٜىٰنْ سَاڧَ دَ غَنْيٜىٰنْ إِظُوابْ، يَڟُواْمَسُ تَرٜىٰ ثِكِنْ جِنِنْ ڟُنْڟُ دَ ضُوً؞ سَعَنً ذَيْ يَيَّڢَا غِدَنْ سَوْ بَݣَويْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zai ɗauki itacen al'ul, da ɗaɗɗoya, da jan alharini, da ɗayan tsuntsu mai ran, ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka a ruwan kaskon, ya yayyafa wa gidan sau bakwai.