Leviticus 14:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sau bakwai zai yayyafa wa mutumin da za a tsabtacce daga cutar mai yaɗuwa ya kuma furta shi tsarkakakke. Sa’an nan ya saki tsuntsu mai rai ɗin ya tafi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَيَيَّڢَا جِنِنْ سَوْ بَݣَويْ عَكَنْ شِے وَنْدَ عَكٜىٰ ڟَبْتَثٜىٰوَ دَغَ مُوغُوَرْ ثُوتَرْ ڢَتَرْ جِكِے؞ بَايَنْ وَنَّنْ سَيْ يَسَنَرْدَ مَيْ ثُوتَرْ ثٜىٰوَ شِ مَرَرْ ڧَظَنْتَا نٜىٰ، كُمَ يَسَكِ ڟُنْڟُ مَيْ رَيْ طِنْ يَتَڢِے دَاجِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya yayyafa jinin sau bakwai a kan wanda za a tsarkake daga kuturtar, sa'an nan ya hurta, cewa, mutumin ya tsarkaka, ya kuma saki tsuntsu mai ran ya tafi cikin saura.