Leviticus 14:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A rana ta bakwai ɗin dole yă aske dukan gashinsa; dole yă aske kansa, gemunsa, gashin girarsa da sauran gashinsa. Dole yă wanke rigunansa ya kuma yi wanka, zai kuwa tsabtacce.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَ تَبَݣَويْ ذَيْ أَسْكٜىٰ دُكَنْ غَاشِنْسَ دَ غَاشِنْ غٜىٰمُنْسَ دَ غَاشِنْ عِدَنُونْسَ، وَتُواْ دُكَنْ غَاشِنْ جِكِنْسَ؞ ذَيْ وَنْكٜىٰ رِيغُنَنْسَ دَ جِكِنْسَ دَ ضُوَ؞ ذَيْ كُوَ كَسَنْثٜىٰ مَرَرْ ڧَظَنْتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A kan rana ta bakwai zai aske dukan gashin kansa, da gemunsa, da gashin girarsa, da duk gashin jikinsa. Sai kuma ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai kuwa tsarkaka.