Leviticus 15:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Idan mace tana ɗigar jini na tsawon kwanaki, ban da kwanakin ganin al’adarta, ko kuwa idan al’adarta ya wuce yawan kwanakin da ya kamata, to, za tă ƙazantu daidai kamar na kwanakin al’adar da ta saba yi. Wato, muddin tana cikin ɗiga, ta zama mai ƙazanta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عِدَنْ مَثٜىٰ تَنَ طِغَرْ جِنِ نَڟَوُانْ ݣُونَكِے، بَنْدَ ݣُونَكِنْ غَنِنْ أَلْعَادَرْتَ، كُواْ كُوَ عِدَنْ أَلْعَادَرْتَ تَا وُثٜىٰ يَوَنْ ݣُونَكِنْدَ يَكَمَاتَ، تُواْ، ذَاتَ ڧَظَنْتُ دَيْدَيْ كَمَرْ يَوَنْ ݣُونَكِنْ أَلْعَادَرْ دَ تَسَابَايِ؞ وَتُواْ، مُدِّنْ تَنَ ثِكِنْ طِغَرْتَ تَڧَظَنْتُ كٜىٰنَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan zubar jinin hailar macen ya yi kwanaki da yawa, ko kuwa kwanakin hailarta sun zarce ka'ida, a duk kwanakin zubar jininta za ta lizima cikin rashin tsarki daidai kamar lokacin hailarta.