Leviticus 15:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk gadon da ta kwanta yayinda ta ci gaba da ɗiga zai zama marar tsarki, kamar yadda gadonta yake a lokacin al’adarta, kuma duk abin da ta zauna a kai zai zama marar tsarki, kamar yadda yake a lokacin al’adarta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ أَبِنْ ݣُونْثِيَرْدَ تَݣُونْتَ عَكَيْ كُواْ تَذَوْنَ عَكَيْ ثِكِنْ ݣُونَكِنْ طِغَرْتَ، ذَيْ ڧَظَنْتُ كَمَرْ نَلُواْكَثِنْ أَلْعَادَرْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kowane gado da ta kwanta a kai a kwanakin zubar jininta, zai zama ƙazantacce, daidai kamar lokacin hailarta. Kowane abin da ta zauna a kai zai ƙazantu kamar a lokacin hailarta.