Leviticus 15:30 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Firist zai miƙa ɗaya saboda hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda ƙazantar ɗigarta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ڢِرِسْتِ يَمِيڧَ طَيَ دَغَ ثِكِنْسُ هَدَايَ تَوَنْكٜىٰ ذُنُوبِ، طَيَنْ كُمَ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا؞ تَهَكَ ڢِرِسْتِ ذَيْ يِڧَٰعِدَرْ ڟَبْتَثٜىٰوَ دُواْمِنْتَ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ، سَبُواْدَ طِغَرْ جِنِنْ دَ تَڧَظَنْتَرْ دَ عِتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Firist ɗin zai miƙa ɗaya hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda rashin tsarkinta.