Leviticus 16:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai ɗibi jinin bijimin da yatsarsa yă yayyafa a gaban murfin kafarar; sa’an nan yă yayyafa jinin da yatsarsa sau bakwai a gaban murfin kafarar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَيْ طِبِے جِنِنْ طَنْ بِجِمِنْ يَيَيَّڢَا شِ دَ يَڟَرْسَ أَغٜىٰڢٜىٰنْ غَبَسْ نَمُرْڢِنْ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ، وَتُواْ أَغَبَنْ عَݣُوتِنْ؞ ذَيْ يَيَّڢَا جِنِنْ أَغَبَنْ مُرْڢِنْ عَݣُوتِنْ سَوْ بَݣَويْ دَ يَڟَرْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya ɗibi jinin bijimin, ya yayyafa da yatsansa a gefen gabas na murfin, zai kuma yayyafa jinin a gaban murfin sau bakwai.