Leviticus 16:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Haruna zai ɗibiya hannuwansa a kan akuya mai ran, yă furta a kansa dukan mugunta da tawayen Isra’ilawa, dukan zunubansu, yă kuma sa su a kan akuyan. Zai kori akuyan zuwa cikin jeji a hannun mutumin da aka ba shi aikin yin haka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَيْسَا حَنُّوَنْسَ بِيُ عَكَنْ كَيْ نَبُنْسُرُ مَيْ رَيْ، يَنَ ڢُرْتَ دُكَنْ لَيْڢُواْڢِنْ یَیَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ دُكَنْ ذُنُبَنْ غَنْ‌غَنْثِنْسُ دَ دُكَنْ ذُنُبَنْسُ؞ تَهَكَ ذَاعَ ظُبَ دُكَنْ ذُنُبَنْ یَیَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ عَكَنْ بُنْسُرُنْ؞ بَايَنْ حَكَ ذَاعَ كُواْرِ بُنْسُرُنْ أَدَاجِ تَهَنُّنْ وَنْدَ عَكَ شِرْيَ دُواْمِنْ وَنَّنْ حِدِمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haruna zai ɗibiya hannuwansa duka biyu a kan kan bunsurun mai rai, ya hurta muguntar Isra'ilawa duka a bisa bunsurun, da dukan laifofinsu, da dukan zunubansu. Zai ɗibiya su a kan kan bunsurun, ya kora shi cikin jeji ta hannun wanda aka shirya zai kora shi.