Leviticus 19:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara ’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَاكُ غِرْبٜىٰ إِنَبِنْكُ كُسَاكٜىٰبِے سَوْ نَبِيُبَ، بَذَاكُ كُمَ تَتَّارَ یَیَنْ إِنَبِنْكُ دَ سُكَ ڢَاطِ ڧَسَابَ؞ ذَاكُ بَرْ وَمَتَلَوْتَ دَ بَڧِنْ دَسُكٜىٰ ذَمَ تَرٜىٰدَكُو؞ نِنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kada ku girbe kalar gonar inabinku, kada kuma ku tattara 'ya'yan inabinku da suka kakkaɓe, sai ku bar wa matalauta, da baƙo. Ni ne Ubangiji Allahnku.