Leviticus 19:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Kada ku yi rashin adalci cikin shari’a; kada ku nuna sonkai ga matalauci, ko ku goyi bayan mai arziki, amma ku shari’anta maƙwabci cikin gaskiya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«بَذَاكُيِ سُوانْكَيْ عَثِكِنْ شَرِيعَبَ؞ بَذَاكُ نُونَ بَمْبَنْثِ وَ تَلَكَاوَا كُواْ كُغِرْمَمَ مَاسُ أَرْزِڧِبَ؞ عَثِكِنْ غَسْكِيَ ذَاكُ شَرْعَنْتَ مَڨُوبْثِنْكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ku yi gaskiya da adalci cikin shari'a, kada ku ma ku yi wa matalauci son zuciya, ko ku goyi bayan mawadaci.