Leviticus 2:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai fid da sashen tunawa daga hadaya ta gari, yă ƙone shi a kan bagade kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتِ ذَيْ طٜىٰبُواْ رَبُواْ نَتُنَاوَا دَغَ هَدَايَ تَهَڟِنْ يَڧُواْنٜىٰشِ عَكَنْ بَغَدٜىٰنْ؞ هَدَايَرْدَ عَكَ مِيڧَ دَ وُتَا كٜىٰنَنْ، مَيْ دَاطِنْ ڧَنْشِ غَ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Firist zai ɗauki kashi na tunawa daga hadaya ta garin, ya ƙona shi bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.