Leviticus 20:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘In mutum ya auri ’yar’uwarsa, ko ’yar mahaifinsa, ko kuwa ta mahaifiyarsa, suka kuma yi jima’i, abin kunya ne. Dole a raba su a idanun mutanensu. Ya ƙasƙantar da ’yar’uwarsa kuma za a nemi hakki daga gare shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عِدَنْ مُتُمْ يَا عَوْرِ یَرْعُوَرْسَ، وَتُواْ یَرْ بَابَنْسَ، كُواْ یَرْ مَامَرْسَ، حَرْ سُكَيِ جِمَاعِ دَ جُونَ، وَنَّنْ أَبِنْ ڧَسْڧَنْثِ نٜىٰ؞ أَغَبَنْ جَمَعَ، ذَاعَ كَوَرْ دَسُو دَغَ جَمَعَرْسُ، غَمَا مُتُمِنْ يَڧَسْڧَنْتَرْ دَ یَرْعُوَرْسَ، أَلْحَكِنْ لَيْڢِنْسَ يَنَ عَكَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Idan mutum ya auri ƙanwarsa ko kuma 'yar mahaifinsa, sai a ƙasƙantar da su a bainar jama'a, a kuwa kore su daga cikin jama'a. Ya kwana da ƙanwarsa ke nan, tilas su sha hukuncin laifinsu.