Leviticus 20:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma na faɗa muku, “Za ku mallaki ƙasarsu, zan ba ku ita gādo, ƙasa mai zub da madara da zuma.” Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya keɓe ku daga al’ummai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا نِے نَا ڢَطَا مُكُ ثٜىٰوَ ذَاكُثِ كُغَاجِ ڧَسَرْسُ؞ ذَنْ بَاكُ عِتَ تَذَمَ مَلَّكَرْكُ، ڧَسَاثٜىٰ مَيْ ظُبَرْدَ مَدَرَ دَ ظُمَ، ڧَسَاثٜىٰ مَيْ أَمْڢَانِ؞ نِنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ وَنْدَ يَوَارٜىٰكُ دَغَ سَوْرَنْ ڧَبِيلُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma ni na faɗa muku, za ku gāji ƙasarsu, zan kuwa ba ku ita, ku mallake ta, ƙasar da take da yalwar abinci. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya keɓe ku daga sauran al'ummai.