Leviticus 20:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku zama tsarkakakke gare ni, gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, na kuma keɓe ku daga al’ummai don ku zama nawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكُ ذَمَ مَاسُ ڟَرْكِے غَرٜىٰنِ، غَمَا نِے يَهْوٜىٰهْ نِے مَيْ ڟَرْكِے نٜىٰ، نَاكُوَ وَارٜىٰكُ دَغَ سَوْرَنْ ڧَبِيلُ دُواْمِنْ كُذَمَ نَوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ku zama tsarkakakku a gare ni, gama ni Ubangiji Mai Tsarki ne, na kuwa keɓe ku daga sauran al'umman duniya don ku zama nawa.