Leviticus 21:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dole su kasance masu tsarki ga Allahnsu, kada kuma su ɓata sunan Allahnsu. Domin sukan miƙa hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta, abincin Allahnsu, saboda haka sai su kasance da tsarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاسُ كَسَنْثٜىٰ دَ ڟَرْكِے غَ اللَّهْ نْسُ، بَذَاسُيِ بَنْظَ دَ سُونَنْ اللَّهْ نْسُ بَ، غَمَا سُونٜىٰ مَاسُ مِيڧَ هَدَايَرْدَ عَكَ مِيڧَ دَ وُتَا غَ يَهْوٜىٰهْ ، وَدَّ تَكٜىٰ عَبِنْثِنْ اللَّهْ نْسُ؞ سَبُواْدَ حَكَ ذَاسُ كَسَنْثٜىٰ دَ ڟَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai su kasance da tsarki, kada su ƙasƙantar da sunana domin su ne masu kawo hadaya ta ci, masu ƙone hadayu da wuta gare ni, don haka sai su kasance da tsarki.