Leviticus 22:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Faɗa musu cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, in wani zuriyarku ya ƙazantu, duk da haka ya kusaci tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka keɓe ga Ubangiji, dole a raba wannan mutum daga gabana. Ni ne Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ نَنْ حَرْ إِيَاكَرْ ڟَارَرَّكِنْكُ، عِدَنْ وَنِ دَغَ ثِكِنْ ذُرِيَرْ ڢِرِسْتُواْثِے يَڧَظَنْتُ عَمَّا يَيِ كُسَدَ بَيٜىٰ بَيٜىٰنَّنْ مَاسُ ڟَرْكِے وَطَنْدَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ كٜىٰٻٜىٰ غَ يَهْوٜىٰهْ ، ذَاعَ كَوَرْ دَشِ دَغَ حِدِمَ أَغَبَنَ؞ نِنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan kowanne daga cikin dukan zuriyarku ya kusaci tsarkakakkun abubuwa, waɗanda Isra'ilawa suka keɓe domina, lokacin da yake ƙazantacce, wannan mutum ba zai ƙara kasancewa a gabana ba, wannan kuwa zai zama har dukan lokatai masu zuwa. Ni ne Ubangiji.