Leviticus 23:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tare da wannan, ku miƙa ’yan raguna bakwai, kowanne bana ɗaya-ɗaya marar lahani, bijimi da kuma raguna biyu. Za su zama hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, tare da hadayunsu na hatsi, da hadayunsu na sha, hadaya da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَطٜىٰ دَ غُرَاسَرْ، ذَاكُ مِيڧَ یَنْ رَغُنَ غُدَا بَݣَويْ مَاسُ شٜىٰكَرَا طَيَ طَيَ مَرَرْ تَبُواْ دَ طَنْ بِجِمِ دَ رَغُنَ بِيُ؞ ذَاكُ مِيڧَسُ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا غَ يَهْوٜىٰهْ تَرٜىٰدَ هَدَايُنْكُ نَهَڟِ دَ نَأَبِنْ شَا، هَدَايَرْدَ عَكَ مِيڧَ دَ وُتَا غَ يَهْوٜىٰهْ ، مَيْ دَاطِنْ ڧَنْشِ غَرٜىٰشِ كٜىٰنَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za su kuma miƙa 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya marasa lahani, da bijimi ɗaya, da raguna biyu tare da abincin. Za a yi hadaya ta ƙonawa da su ga Ubangiji, tare da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, wato, hadaya ta ƙonawa da wuta, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.