Leviticus 23:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Firist zai kaɗa ’yan raguna biyun a gaban Ubangiji, a matsayin hadaya ta kaɗawa, tare da burodin sababbin ’ya’yan fari na itatuwan. Tsarkaken hadaya ce ga Ubangiji ga firist.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتِ ذَيْ طَغَ یَنْ رَغُنَنَّنْ بِيُ حَطٜىٰ دَ غُرَاسَ نَنُونً ڢَارِ هَدَايَ تَطَغَوَ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ أَنْ كٜىٰٻٜىٰسُ دَ ڟَرْكِے غَ يَهْوٜىٰهْ ، رَبُواْ نَڢِرِسْتِنٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Firist zai kaɗa su tare da abinci na nunan fari domin hadaya ta kaɗawa, da 'yan ragunan nan biyu a gaban Ubangiji. Za su zama tsarkakakku ga Ubangiji domin a ba firist.