Leviticus 23:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Rana ta goma ta wata bakwai, za tă zama Ranar Kafara. Sai ku yi taro mai tsarki don ku yi mūsun kanku ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«رَانَ تَغُواْمَ غَ وَتَ نَبَݣَويْ ذَاتَ ذَمَ رَانَرْ طَوْكَرْ أَلْحَكِنْ ذُنُوبِ؞ ذَاتَ ذَمَ مُكُ رَانَرْ تَارُواْ مَيْ ڟَرْكِے؞ ذَاكُيِ أَظُمِ كُيِ هَدَايَرْدَ عَكَ مِيڧَ دَ وُتَا غَ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
rana ta goma ga watan bakwai za ta zama rana ta yin kafara da lokacin yin muhimmin taro. Kada su ci abinci a ranar, su taru su yi sujada, su miƙa hadaya taƙonawa ga Ubangiji.