Leviticus 23:40 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A rana ta fari, za ku ɗebi zaɓaɓɓun ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, da rassan dabino, rassa masu ganye, da kuma ganyayen itacen wardi na rafi, ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, kwana bakwai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَ تَڢَرْكُوانْ، ذَاكُ طِبِے یَیَنْ إِتَاثٜىٰ نَ عِتَتُوَ مَاسُ ݣَوْ دَ رَسَّنْ إِتَاثٜىٰنْ دَبِينُواْ دَ رَسَّنْ عِتَتُوَ مَاسُ غَنْيَيٜىٰ دَيَوَ دَ رَسَّنْ عِتَتُوَ نَبَاكِنْ رَاڢِ، كُيِتَيِنْ مُرْنَ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ حَرْ ݣُونَ بَݣَويْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ranar sai su ɗibi 'ya'yan itatuwa masu kyau, da rassan dabino, da kauraran rassan itatuwa masu ganye, da itacen wardi na rafi, sa'an nan su nuna bangirma gaban Ubangiji Allahnsu har kwana bakwai.