Leviticus 24:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ka kai mai saɓon nan waje da sansani. Duk waɗanda suka ji maganar da mai saɓon nan ya yi su ɗibiya hannuwansu a kansa, taron jama’a kuwa gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كَطَوْكِ مُتُمِنْ دَ يَيِ صَاٻُوانْ ذُوَا بَايَنْ ذَنْغُوانْ؞ كَسَا دُكَنْ وَطَنْدَ سُكَجِ صَاٻُوانْدَ يَيِ سُسَا حَنُّوَنْسُ عَكَنْ كَنْسَ، سَعَنً أَسَا دُكَنْ جَمَعَ سُجٜىٰجّٜىٰڢٜىٰشِ دَ دُوَڟُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Fito da wanda ya yi saɓon nan daga cikin zangon. Ka kuma sa dukan waɗanda suka ji shi su sa hannuwansu a bisa kansa. Taron jama'ar kuwa su jajjefe shi da duwatsu.