Leviticus 24:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
duk wanda ya saɓi sunan Ubangiji, dole a kashe shi. Dole jama’a gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu. Ko baƙo, ko haifaffen ɗan ƙasa, sa’ad da ya saɓi Sunan Ubangiji, dole a kashe shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُمَ دُكْ وَنْدَ يَسَٻِ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ ، ذَاعَ كَشٜىٰشِ؞ دُكَنْ جَمَعَ ذَاسُ جٜىٰجّٜىٰڢٜىٰشِ، كُواْ دَشِے بَڧُواْ نٜىٰ كُواْ طَنْ ڧَسَرْ نٜىٰ؞ سَعَدَّ مُتُمْ يَسَٻِ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ ، ذَاعَ كَشٜىٰشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
za a kuwa kashe shi. Duk Ba'isra'ile ko baƙon da yake zaune cikin Isra'ilawa wanda ya saɓi Allah, sai taron jama'a su jajjefe shi da duwatsu ya mutu.