Leviticus 24:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wannan burodin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza, waɗanda za su ci a tsattsarkan wuri, gama sashe ne mafi tsarki na rabonsu na kullum na hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ غُرَاسَرْ ذَيْ ذَمَ رَبُوانْ هَٰرُونَ دَ نَیَیَنْسَ مَظَا؞ ذَاسُثِ أَوَنِ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے، غَمَا وَنَّنْ رَبُواْ يَنَدَ ڟَرْكِے سُواْسَيْ دَغَ ثِكِنْ هَدَايُنْ دَ عَكَ مِيڧَ دَ وُتَا غَ يَهْوٜىٰهْ ؞ وَنَّنْ ڧَٰعِدَ ثٜىٰ تَدِنْدِنْدِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan abinci zai zama rabon Haruna da na 'ya'yansa maza, za su ci a wuri mai tsarki, tun da yake a gare shi rabo ne mai tsarki daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji. Wannan farilla ce har abada.