Leviticus 25:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku keɓe shekara ta hamsin ku kuma yi shelar ’yanci a dukan ƙasar ga mazaunanta. Za tă zama shekarar murna gare ku; kowannenku zai koma ga mallakar iyalinsa, kuma kowa ga danginsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاعَكٜىٰٻٜىٰ وَنَّنْ شٜىٰكَرَا تَهَمْسِنْ دَ ڟَرْكِے؞ ذَاعَكُوَيِ شٜىٰلَرْ سَامُنْ یَنْثِ أَدُكَنْ ڧَسَرْ غَ دُكَنْ مَذَوْنَنْتَ؞ ذَاتَ ذَمَ شٜىٰكَرَا تَسَامُنْ یَنْثِ أَغَرٜىٰكُ؞ كُواْوَ ذَيْكُواْمَ غَ كَايَنْ غَادُوانْ عِيَلِنْسَ، كُواْوَ كُمَ غَ عِيَلِنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Shekara ta hamsin kuwa za su keɓe ta, su yi shelar 'yanci cikin ƙasar duka ga dukan mazaunanta. Za ta zama shekarar murna a gare su. Kowa zai koma mahallinsa, ko wannensu kuma wurin danginsa.