Leviticus 25:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da mutum ya sayi fili daga abokin zamansa, kuɗin zai kasance bisa ga yawan shekara hamsin ta murna da suka wuce, da kuma bisa ga yawan shekarun noma da suka rage kafin wata shekara hamsin ta murna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ مُتُمْ يَسَيِ ڢِيلِ دَغَ مَڨُوبْثِنْسَ، كُطِنْ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ بِسَغَ يَوَنْ شٜىٰكَرُنْ دَ سُكَ وُثٜىٰ بَايَنْ شٜىٰكَرَا تَهَمْسِنْ تَسَامُنْ یَنْثِ دَ كُمَ بِسَغَ يَوَنْ شٜىٰكَرُنْ نُواْمَ وَطَنْدَ سُكَ رَغُ كَاڢِنْ وَتَ شٜىٰكَرَا تَهَمْسِنْ تَسَامُنْ یَنْثِ تَكٜىٰوَيُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan za ka yi sayayya a wurin maƙwabcinka, sai ka lura da yawan shekarun da za ka mora kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo.