Leviticus 25:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Idan shekarun suna da yawa, sai ku kara kuɗin filin, idan kuma shekarun ba su da yawa, sai ku rage kuɗin filin, gama ainihin abin da ake sayar maka shi ne yawan hatsin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ شٜىٰكَرُنْ دَ سُكَ رَغُ كَاڢِنْ وَتَ شٜىٰكَرَا تَهَمْسِنْ تَسَامُنْ یَنْثِ سُنَدَ يَوَ، كُطِنْ ڢِيلِنْ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ دَيَوَ؞ عِدَنْ شٜىٰكَرُنْ دَ سُكَ رَغُ كَاڢِنْ شٜىٰكَرَا تَهَمْسِنْ تَسَامُنْ یَنْثِ بَسُ دَيَوَ، حَكَمَا كُطِنْ ڢِيلِنْ بَذَيْ يِيَوَبَ؞ غَمَا أَنَ سَيَرْ مَكَ بِسَغَ شٜىٰكَرُنْ دَ ذَاكَثِ أَمْڢَانِنْسَ نٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan shekarun sun ragu da yawa kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo, sai ka saya da tsada. Idan kuwa shekarun sun ragu kima ne, sai ka saya da araha, gama yana sayar maka bisa ga yawan shekarun da za ka mora ne.