Leviticus 25:28 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma in bai sami halin sāke biyansa ba, abin nan da ya sayar zai ci gaba da zama mallakar mai sayan, sai Shekara ta Murna. Za a maido masa da ita a Shekara ta Murna, sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا عِدَنْ بَاشِ دَ إِسَشّٜىٰنْ أَبِنْدَ ذَيْڢَنْشِ أَبِنْسَ، تُواْ، ڢِيلِنْ دَ عَكَ سَيَرْ دَشِ ذَيْثِيغَبَ دَ ذَمَ أَ حَنُّنْ وَنْدَ يَسَيَ حَرْ سَيْ شٜىٰكَرَا تَهَمْسِنْ تَسَامُنْ یَنْثِ؞ أَوَنَّنْ شٜىٰكَرَنٜىٰ، ذَاعَ مَيَرْوَ عَيْنِحِنْ مَيْ ڢِيلِنْ دَ ڢِيلِنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma idan ba shi da isasshen abin da zai fanshi abinsa, to, sai wanda ya karɓi jinginar ya ci gaba da riƙon abin da aka jinginar masa ɗin har shekara ta hamsin ta murna, a lokacin ne zai mayar wa mai shi, mai shi ɗin kuwa ya koma a kan mahallinsa.