Leviticus 25:30 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In ba a fanshe shi a ƙarshen shekara ba, gidan da yake a birni mai katanga, zai zama mallakar na ɗinɗinɗin na mai sayan da kuma zuriyarsa. Ba za a mai da shi a Shekara ta Murna ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا عِدَنْ بَيْ عِيَ ڢَنْسَرْ غِدَنْ ثِكِنْ شٜىٰكَرَا غُدَنَّنْ بَ، تُواْ غِدَنْ دَيَكٜىٰ عَثِكِنْ بِرْنِ مَيْ كَتَنْ‌غَ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ دِنْدِنْدِنْ نَوَنْدَ يَسَيَ، حَرْ إِيَاكَرْ ڟَارَرَّكِنْسَ؞ بَذَاعَ مَيَرْدَ غِدَنْ أَ شٜىٰكَرَا تَهَمْسِنْ تَسَامُنْ یَنْثِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan kuwa bai fanshi gidan a ƙarshen shekara guda ba, sai gidan nan da yake cikin birni mai garu ya zama mallakar wanda ya karɓi jinginar, da na zuriyarsa duka har abada. Ba za a mayar wa maigidan da gidan a shekara ta hamsin ta murna ba.