Leviticus 25:31 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma za a ɗauki gidaje a ƙauyuka marasa katanga kewaye da su daidai da gonaki. Za a iya fanshe su, a kuma mayar da su a Shekara ta Murna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا غِدَاجٜىٰ نَڧَوْيُكَ عِنْدَ بَابُ كَتَنْ‌غَ كٜىٰوَيٜىٰ دَسُو، ذَاعَ لِسَّڢْتَاسُ كَمَرْ ڢِيلَيٜىٰنْ غُواْنَكِ نٜىٰ؞ ذَاعَ عِيَ أَ ڢَنْشٜىٰسُ، ذَاعَ كُمَ مَيَرْوَ عَيْنِحِنْ مَاسُ غِدَاجٜىٰنْ أَ شٜىٰكَرَا تَهَمْسِنْ تَسَامُنْ یَنْثِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma gidajen da suke cikin ƙauyuka da ba su cikin garu, sai a lasafta su daidai da gonakin da suke cikin ƙasar, ana iya fansarsu, za a kuma mayar wa masu su a shekara ta hamsin ta murna.