Leviticus 25:46 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za ku iya ba da su ga ’ya’yanku a matsayin kayan gādo, za ku kuma iya mai da su bayi dukan rayuwarsu, amma kada ku yi mulki a bisa ’yan’uwanku Isra’ilawa da tsanani.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكَ عِيَ مَيْشٜىٰسُ أَبِنْ غَادُواْ غَ یَیَنْكَ دُواْمِنْ سُذَمَ مَلَّكَرْ یَیَنْكَ؞ ذَاسُ ذَمَ مُكُ بَايِ نَدِنْدِنْدِنْ؞ عَمَّا غَمٜىٰدَ یَنْعُوَنْكُ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا، وَنِ بَذَيْ يِمُلْكِ عَكَنْ وَنِ تَرٜىٰدَ نُونَ مَسَ عَذَابَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kwa iya barinsu ga 'ya'yanku maza a bayanku su gāda, su zama abin mallakarsu har abada. Kwa iya bautar da su, amma 'yan'uwanku, Isra'ilawa, ba za ku mallaki juna da tsanani ba.