Leviticus 25:50 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da shi da mai sayansa, za su ƙirga lokaci daga shekarar da ya sayar da kansa har zuwa Shekara ta Murna. Farashin sakinsa zai dangana a kuɗin da ake biyan ma’aikacin da aka ɗauka aiki, na yawan shekarun ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
شِے دَ وَنْدَ يَسَيٜىٰشِ ذَاسُ لِسَّڢْتَا يَوَنْ كُطِنْ؞ يَوَنْ كُطِنْ دَ ذَاعَ بِيَ دُواْمِنْ یَنْثِنْسَ ذَاعَ لِسَّڢْتَا بِسَغَ يَوَنْ شٜىٰكَرُنْ دَ سُكَ رَغُ كَاڢِنْ شٜىٰكَرَا تَهَمْسِنْ تَسَامُنْ یَنْثِ تَكٜىٰوَيُواْ؞ ذَاعَيِ لِسَّڢِنْ بِسَغَ كُطِنْ دَ عَكٜىٰ بِيَنْ لٜىٰبُرَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya sa wanda ya saye shi ya lasafta tun daga shekarar da ya sayar da kansa, har zuwa shekara ta hamsin ta murna. Ƙuɗin da za a fanshe shi zai zama daidai da yawan shekarun da suka ragu kafin shekara ta murna. Sai a ɗauke shi kamar bara na ijara.