Leviticus 26:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutanenku biyar za su kori mutum ɗari, mutanenku ɗari kuma za su kori mutane dubu goma, abokan gābanku kuma za su fāɗi a kaifin takobi a gabanku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْكُ بِيَرْ ذَاسُ كُواْرِ مُتَنٜىٰنْسُ طَرِے، مُتَنٜىٰنْكُ طَرِے كُوَ ذَاسُ كُواْرِ مُتَنٜىٰنْسُ دُبُو غُواْمَ؞ ذَاكُ بُغِ أَبُواْكَنْ غَابَنْكُ دَ تَكُواْبِے سُڢَڢَّاطِ أَغَبَنْكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutum biyar ɗinku za su runtumi mutum ɗari, mutum ɗari ɗinku za su runtumi mutum dubu goma. Maƙiyanku kuwa za su fāɗi a gabanku ta kaifin takobi.