Leviticus 27:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In mutumin da ya keɓe gidansa ya fanshe shi, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar, gidan kuma zai zama nasa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ شِے وَنْدَ يَكٜىٰٻٜىٰ غِدَنْ يَنَ سُواْ يَڢَنْشِ غِدَنْ، سَيْ يَڧَارَ كَشِ طَيَ ثِكِنْ بِيَرْ عَكَنْ أَبِنْدَ عَكَ ڟَارَا؞ غِدَنْ كُوَ ذَيْ ذَمَ نَاسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan shi wanda ya keɓe gida nasa yana so ya fansa, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin da aka kimanta, gidan kuwa zai zama nasa.